Komitin karɓar mulki a jihar Kano ta zargi Gwamna Ganduje da kin bada damar tattaunawa da komitin karɓar mulki da sabon Gwamna mai jiran gado ya kafa.
Da yake zantawa da manema labarai shugaban komitin karɓar mulki Dr Bappah Bichi ya koka ga yadda Gwamnan yake kafar ungulu ga komitin ta hanyar kin bada dama ga komitin da yace ya kafa don fara tattaunawa da su.
Komitin karɓar mulki a jihar Kano ya yanke shawarin fara tattaunawa da sakatarorin dindindin na ma’aikatun gwamnatin jihar kano don tunkarar aikin da yake gaban su.