Ƙasar Saudiyya ta duƙufa wajen tsara biki na musamman domin karrama mai girma gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje a dalilin namijin ƙoƙarinsa wajen musuluntar da maguzawa sama da mutum dubu goma batare da zubar da jini ba.
A cewar mahukuntar ƙasar, abin da gwamna Gandujen ya yi wata babbar gudunmawa ce ga addinin musulunci wacce babu wani ɗan siyasa da ya taɓa ba da irinta a Afrika ta yamma gaba ɗaya a wannan ƙarni na 21 tayadda hakan ke nuni da yadda gwamnan ya cancanci yabo.
Ƙasar ta Saudiyya ta kuma ƙara da cewa a dalilin wannan ƙoƙari da gwamna Ganduje ya yi, za ta rubuta sunansa a cikin kundin tarihinta wanda ta samar domin rubuta sunayen mutanen da ke ba wa musulunci gudunmawa mai girma a Nahiyar Afrika.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da ƙasar ta Saudiyya ta ke yabawa gwamna Ganduje a kan ƙoƙarinsa na hidimtawa addinin musulunci ba, ko da a baya ta taɓa karrama shi da lambar yabo mai ɗauke da ƙyallen ɗakin Ka’aba.
Sai dai a wannan karon a na tunanin salon karramawar zai sha bamban da duk wanda aka taɓa yi masa a baya girma domin kuwa gagarumin biki ne na musamman wanda ake za ra halartar manyan shugabanni na duniya.