Daga Zailani Mustapha
Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky a Zariya ta jihar Kaduna sun koka bisa yadda gwamnatin jihar Kaduna mai barin gado a karkashin gwamna Nasir El-Rufai ta rushe wani gidan marayu da aka gina sama da shakaru 54 da suka gabata a Anguwar Babban Dodo dake garin Zariya.
Wannan kukan ya fito ne daga bakin Abdulhamid Bello wanda shi ne wakilin ‘yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky na garin Zariya da kewaye a taron manema labarai da ya kira da yammacin ranar Litinin 28 ga watan Mayun 2023. Wakilinmu na daya daga cikin kafafen watsa labarai da suka kasance a taron.
Abdulhamid Bello ya ce da asubahin ranar Lahadi da misalin karfe 4 ne jami’an tsaro da na KASUPDA suka iso gidan marayun inda suka rushe shi ba tare da wani notis ko sanarwa ba.
“kamar yadda aka sani wannan gwamnatin bisa jagorancin Nasir El-Rufai sun zo ne suka yi wani abu wanda za a ce masa mummunan ta’addanci. Ta’addanci akan dukiyar marayu. Saboda wannan gidan da suka rusa da asuba gida ne mallakin Marigayi Alhaji Hamidu Danlami, sanannen dan kasuwa a nan Zariya. Kuma wannan gini ya haura shekara 54. Sannan marigayi ya koma ga Allah, ya zama gida ne na magadansa, suka zo suka rusa wannan gida gaba daya”, ya nusasshe.
Shehin Malamin ya ci gaba da cewa abin ban mamakin ma jami’an ba su tsaya ga gidan kawai ba, sun rusa harda masallacin da marigayin ya gina wanda ake amfani da shi ana sallah; “kamar yadda kuke gani shima sun bi sun rusa shi ba tare da nau’in sanarwa ba”, ya nusasshe.
Ya ci gaba da cewa ba ya ga wannan sun kuma je wani kauyen Bomo sun rusa wata makarantar Fudiyyah. “wannan abin ne idan ma ana kallon makaranta kayan al’umma ne wanda ta yiwu a ce ko mallakin wasu ‘yan kungiya ko jama’a, to gida ne fa? Mallakin jama’a ne? Ko mutum ba zai mallaki gida bane? Ko kuma idan ya rasu ya bar wa magada shi ke nan a zo a rusa shi? Ko rusa gida shi ne rusa akidar mutane? Sannan mene ne laifin masallacin da ake sallah a ciki aka rusa shi?” ya tambaya.
Shehin Malamin ya lurantar da yadda sakamakon zuwa rushe-rushen aka firgita al’umma ta hanyar jefa tiyagas a anguwar. “wurin ma yanzu haka bai shigowa saboda hayakin tiyagas”, ya labarta.
Kuma za su nemi hakki a gaban hukumar shari’a bisa wannan rushe-rushen da aka yi; “da sauran ma wasu matakai wanda ba lalai ne sai ma mun bayyanar ba amma mataki kam akwai matakai. Domin wannan ta’addancin ba zai wuce da shi ba. Ai gobe iwarhaka ba sunan shi gwamna ba. Idan kuma sabon gwamnati za ta dauki irin salonsa to shi ke nan bismillah. Yadda shi ya yi shekaru takwas ya yi ta’addanci bai yi nasara ba, wannan shima zai kammala shekarunsa takwas idan har zai dauki wannan salo ba inda zai je. Domin ta’addanci ba zai taba kauda mutane akan abin da suka yi imani ba”, ya jaddada.
Sai dai ya ce duk da wannan rushe-rushe da gwamnati mai barin gado ke yi, hakan ba zai sanyaya musu guiwa bisa abin da suka yi imani da shi ba illa ma kara musu kwarin guiwa hakan zai yi.
“karin karfi ma wannan ke kara mana. Yanzu misali idan ka duba tunda safe al’ummar da suke zuwa nan mutane hawaye suke yi. Mutane ma wanda abin bai shafe su ba tausayawa suke, ina kuma gare mu. Yawwa magabatanmu fiye da wannan. Wanda yake ganin cewa sabooda kiyayyarsa ga addini zai yi mana wannan, sai mu ce ya ci gaba. Fir’aunonin da suka fi shi karfin mulki ba su yi nasara a zamaninsu ba, shima mun tabbatar da cewa ba tsinana komai ba sai dai ya yi hasara duniya da lahira, mune za mu yi nasara”, ya jaddada.
A karshe ya nemi almajiran Shaikh Zakzaky da su ci gaba da tsayawa kan gaskiya da adalci tare da nuna juriya da hakuri, inda ya ce Allah zai taimaki mai gaskiya. Ya ce su kuma masu zaluntarsu akwai ranar kin dillanci; “duk abin da suka yi ba za a manta da shi ba, za a rama. Yanzu wadannan yaran gidan nan da aka zo aka rusa musu dukiya aka sa su kuka a ce wai yanzu su manta da wannan ta’addancin? Ba za mu yafe wannan ba. Saboda haka su tara laifukan tun ma a nan duniya kafin a je gaba ga Allaha za su gamu da gamuwarsa”, ya lurantar.
Ya kuma ja hankalin al’umma da cewa su daina yin shiru ga zalunci, domin a cewarsa yin shiru ga zalunci taimakon zalunci ne. Kuma abu ne da Allah ta’ala ya hana.
Wakilinmu da ya halarci wuraren da aka rusa ya shaida yadda aka rushe gidan marayun, masallaci da kuma makaranta.