A shekarun 1950, lokacin da tarayyar soviet ke kokarin ganin ta isa duniyar wata, masana kimiya a Amurka sun yi kokarin kaddamar da wani shiri – na amfani da wata domin firgita tarayyar.
A lokacin da dan saman jannati, Neil Armstrong ya dawo daga duniyar wata a 1969, ya kasance yanayi na tarihin da duniya ke tunawa.
Sai dai da ace Armstrong ya dawo da burbushin da zai kasance guba sakamakon makaman nukiliyar da aka rinka harbawa fa?
A lokacin karanta wata makala a karon farko – Da ke bayyani kan binciken wata – kowa ya yaba da hikimar da aka zuba cikin kwanciyar hankali. Makalar da kowa ke iya kau da kai. Kuma kusan haka ne ya kasance.
Amma da zaran mutum ya natsu, abubuwan da ke kunshe a bayanai sun sha bamban.
Shirin A119, kamar yada ake kiransa, wani shiri ne na sirri kan yada za a yi amfani da makamin nukiliyyar Hydrogen a tarwatsa wata.
Nukiliyyar Hydrogen na da hadari gaske domin karfinsa ya zarta nukiliyar da aka harba a Hiroshima a 1945, kuma a wannan lokaci shi ne makami na nukiliya da aka kera.
A wannan lokaci tsakanin watan Mayun 1958 zuwa Janairun 1959 babban jami’in sojan sama, Reiffel ya yi ta kai koma kan tabbatuwar shirin.
Duk da cewa binciken nasu na iya amsa wasu tambayoyi kan wata, shirin A119 an tsara shi ne domin wannan aiki.
An tsara bam din ya tarwatse tsakanin wuri mai duhu da haske a jikin wata – domin kowa ya ga karfin hasken fashewar wata, musamman a Kremlin.
Abu guda ke iya gamsarwa ko bada hujja kan dalilan wannan shiri mai hadari kuma maganar ba ta zarce batun tsaro da zakuwa ba.
A 1950 babu alamar da ke nuna Amurka za tayi nasara a yaki. Ra’ayoyin ‘yan siyasa da fitattun mutane a Amurka sun nuna cewa Tarayyar Soviet na kan gaba a bunkasar nukiliya, musamman wajen cigaba, da adadin makaman da makami mai linzami.
A 1952, Amurka ta fasa makamin nukiliyan hydrogen na farko. Bayan shekara uku Tarayyar Soviet ta kidimar da Washington bayan gwada nata makamin.
A 1957 sun sake samun cigaba, da kwace ragamar sararin samaniya bayan kaddamar da Sputnik 1, tauraron dan adam na farko da ke zageye duniya.
Hakan bai taimaki Amurka cewa an kaddamar da Sputnik bayan makami mai linzami na Tarayyar Soviet ba, kuma ba wai ya nuna Amurka tayi kokari amfani da damar wajen tarwatsa wata ba ne.
An ta nuna bajintar da aka nada a fadin duniya
A shekarar 2000, Reiffel ya taba cewa ba dan tangadar da aka samu ba, da duniya ta shaida fashewar makamin da aka tura wata.
Wannan wani abin damuwa ne ga muhalli da kuma sojojin Amurka duk da cewa masana kimiya a wancan lokaci na da kwarin-gwiwa.
Shirin A119 na daya daga cikin shirye-shirye da ke zama kamar martani bayan harba Sputnik, a cewar Alex Wellerstein, masanin tarihi da makamin nukilliya.
A ganinsa harba Sputnik, abu ne daya burge don haka basa nadamar nasu gwajin.
Abin da suka yi a karshe, shi ne harba nasu na’urar, da dan jinkirtawa, amma fa ba su hakura ba, domin su ci gaba da gwadar sa’arsu har zuwa karshen shekarun 1950.
Abin al’ajabi ne, la’akari da tunanin Amurka a wannan lokaci.
Wannan wani yanayi ne da ke nuna abubuwan mamaki da kuma burgewa da suke kokarin gwada sa’arsu.
”Ina ganin a wannan gabar kalmar burgewa da tsoratarwa duk na iya kayatarwa”
Bai tabbatar da tunanin da aka hada wajen bijiro da wannan shiri ba. Amma duk wanda ya kasance cikin tsarin yana da bai wa da zurfi tunani, a cewarsa.
Ba su damu da aikin ba, kuma babu tsoro a tattare da su na abin da zai iya jawo wa milyoyin mutane a duniya.
Masana kimiya da dama su gwada abubuwa daban-daban, sai dai a wani lokaci suna yarda da cewa lissafin nasu siyasa na tasiri sosai a ciki.
Rahoton BBC Hausa