Daga: Saliedeen Sicky
Birtaniya ta kwace iko da wannan yanki da ake kira Falasdinu bayan da aka ci Daular Usmaniyya, wadda wannan yankin na Gabas ta Tsakiya ke karkashin ikonta a lokacin, a yakin duniya na daya. A lokacin Yahudawa ne ‘yan kadan da kuma Larabawa da ke da rinjaye ke zaune a yankin.
Rikici ya fara tashi a lokacin da manyan kasashen duniya suka bai wa Birtaniya ikon kafa abin da suka kira kasar Yahudawa a wurin. Yahudawa sun ce kasar kakanninsu ta asali ne, kamar yadda su ma Larabawan Falasdinu ke ikirari suka kuma ki wannan shiri na kafa kasar Yahudawa a wurin.
Tsakanin shekarun 1920 da shekarun 1940 yawan Yahudawan da ke komawa can ya karu, inda yawancinsu suke gudu daga gallazawar da ake musu a Turai bayan kisan-gillar Yahudawa na yakin duniya na biyu. Haka kuma tashin hankali tsakanin Yahudawa da Larabawa a kan kin yarda da mulkin Birtaniya ya karu.
A 1947 Majalisar Dinikin Duniya ta kada kuria’r raba yankin na Falasdinu biyu inda za a kafa kasar Isra’ila da kuma ta Larabawa, yayin da birnin Kudus zai kasance na duniya wato mallakar kasashen biyu. Shugabannin Yahudawa sun amince da wannan tsari yayin da na Larabawa suka yi watsi da shi, inda aka kasa aiwatar da shi.
Kafa kasar Isra’ila da korar Falasdinawa
Lokacin da mahukuntar Birtaniya suka kasa shawo kan matsalar a 1948, sai suka fice suka tafi, daga nan sai shugabannin Yahudawa suka yi amfani da wannan dama suka kafa kasar Isra’ila. Falasdinawa da dama suka ki yarda da hakan sai kawai yaki ya biyo baya. Dakaru daga kasashen Larabawa masu makwabtaka sai suka shigo su ma suka yi mamaya.
Bayan da yaki ya yi yaki, dubban Falasdinawa sun tsere ko kuma an tilasata musu barin gidajensu a abin da suka kira Al Nakba.
Zuwa lokacin da aka gama yakin da yarjejeniyar dakatar da bude wuta a wannan shekara, Isra’ila ta kame mafi yawan yankunan.
Yankin da Jordan ta kama ya zama Gabar Yammacin Kogin Jordan, wanda Masar ta kama kuma ya zama Gaza. An raba Kudus tsakanin sojojin Isra’ila a Yamma da kuma na Jordan a Gabas. Kasancewar an kawo karshen yakin ne ba tare da wata cikakkiyar yarjejeniya ba an ci gaba da yakin daga lokaci zuwa lokaci inda kowane bangare ke dora wa daya bangaren laifi a gomman shekaru.
A wani yakin kuma na 1967, Isra’ila ta mamaye Gabashin Isra’ila da Gabar Yammacin Kogin Jordan da kuma yawancin Tuddan Golan hadi da Gaza da kuma tsibirin Sinu na Masar. Yawancin ‘yan gudun hijirar Falasdinu suna zaune a Gaza da Gabar yamma da kuma yankunan kasashen Jordan da Syria da kuma Lebanon.
Tun daga sannan Isra’ila ta hana wadannan Falasdinawa ko ‘ya’aynsu komawa su zauna a yankunansu. Isra’ila ta kafe a kan haka ne da cewa za su mamaye kasar, wanda hakan zai zama barazana ga wanzuwar kasar Yahudu.
Har yanzu Isra’ila ce ke mamaye da Gabar Yamma, kuma duk da cewa ta fice daga Gaza, Majalisar Dinkin Duniya tana daukar wannan yankin a matsayin wanda Isra’ila ta mamaye. Isra’ila na ikirarin cewa dukkanin Birnin Kudus babban birninta ne yayin da Falasdinawa ke cewa Gabashin Birnin shi ne zai kasance babban birnin kasarsu idan aka kafa ta.
Amurka ce kasa daya tilo daga cikin ‘yan kalilan din da suka amince da birnin a matsayin babban birnin Isra’ila. A cikin shekara 50 da ta gabata Isra’ila ta gina gidajen Yahudawa a wadannan yankuna inda a yanzu ake da Yahudawa sama da 60,000.
Falasdinu na cewa wannan ya keta ka’idar dokokin duniya kuma tarnaki ne ga zaman lafiya, amma kuma Isra’ila na musanta hakan.
Me yake faruwa yanzu?
Yawanci ana zaman dar-dar da samun tashin hankali a tsakanin Isra’ila da Falasdinawan da ke zaune a Gabashin Birnin Kudus da Gaza da kuma Gabar Yamma da Kogin Jordan. Kungiyar gawgawramayar Falasdinawa ta Hamas wadda a lokuta da dama take yakar Isra’ila ita ce ke mulkin Gaza.
Hukumomin Isra’ila da na Masar na tsananta iko da iyakar Gaza domin hana makamai kaiwa ga Hamas. Falasdinawan da ke zaune a Gaza da Gabar Yamma na kokawa da mawuyacin halin da suka ce suna ciki saboda matakin Isra’ila na tsaro a iyakar.
Ita kuwa Isra’ila na cewa tana yin hakan ne domin kare kanta daga abin da ta kira tashin hankalin Falasdinawa.
Yunkurin korar wasu Falasdinawa daga Gabashin BIrnin Kudus ma na tayar da rikici.
Wadanne ne manyan matsalolin?
Shi dai wannan rikici ba abu ne da ake ganin za a iya magance shi ba nan da wani dan lokaci.
Shirin wanzar da zaman lafiya na baya-bayan nan da Amurka ta samar a lokacin mulkin Donald Trump wanda tsohon Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yaba da shi bai samu karbuwa ba wajen Falasdinawa, saboda sun bayyana shi da cewa ya fifita bangare daya
Saboda haka duk wata yarjejeniyar zaman lafiya da za a yi nan gaba dole ne ta samu karbuwa wajen bangarorin biyu.
Editan BBC na yankin Gabas ta Tsakiya Jeremy Bowen, ya ce rikicin watan Mayu na 2021 shi ne yaki na hudu mafi girma tsakanin Hamas da Isra’ila tun 2008. Editan ya ga yaki da dama da ya kare kamar wannan a baya, inda kowa ne bangare ke ikirarin samun nasara. Amma kuma nan da nan sai a dasa dan-ba na wani sabon rikicin.
Ya ce, ”Ina tabbatar ma da cewa in dai ba a sauya tsarin da ake ciki ba a yanzu, to ba shakka wani yakin zai sake barkewa.”
Abin da ke zahiri ya tankwaɓe fatan zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Palasɗinawa
Tashin hankalin da ke faruwa tsakanin Isra’ila da Palasdinawa na kara ta’azzara, inda fatan da ake da shi na samun zaman lafiya da warware matsalolin da ke tsakanin bangarorin biyu ke da kamar wuyar faruwa.
Kudus birni ne mai tsarki ga wadanda suka yi imani da hakan.
Yanayin wurin a nan kan kasance cike da karar hayaniya mai karfi a lokacin da mabiya ke bikin hutun addini, musamman ma a tsohon birnin mai zagaye da bango inda wurare masu tsarki na Kiristoci da Yahudawa da Musulmai suka kasance ga baki-ga-hanci da juna. Addini na da wani muhimmanci da kuma karfi a nan da yake da matukar wahala a iya kururutawa.
Hakan kuwa saboda ya shafi addini fiye da daya kawai. A birnin Kudus ana danganta shi da Palasdinu da Isra’ila. Addini, da siyasa da asali na yin tasiri ga juna. Bangarorin biyu masu gogayya da juna na girmama tsarkakar birnin na Kudus tare da ikirarin cewa babban birnin su ne.
A wannan watan Ramadan Daya Wuce da bukukuwan Passover na Yahudawa da na Easter na Kiristoci sun zo a lokaci guda. Sun kuma zo a daidai lokacin karuwar yanke kauna da kuma fargaba da hadari.
Shekaru biyu da suka gabata, tsaurara dokokin Isra’ila a kan Palasdinawa lokacin watan Ramadan na daya daga cikin abubuwan da suka rura wutar tashin hankali mai muni ne a yankin Gaza tsakanin Yahudawa da kungiyar Hamas ta Palasdinawa, Ya nuna alamun kamar akwai yiwuwar hakan zai sake faruwa a cikin watan Na Ramadan, lokacin da jami’an tsaron Isra’ila suka kutsa cikin Masallacin al- Aqsa, inda Musulmai suka yi amanna nan ne Annabi Muhammadu (SAWW) ya hau zuwa aljanna.
‘Yan sanda sun yi amfani da dabaru na mugunta wajen fitar da Palasdinawa da suka kulle kansu a cikin masallacin.
Hoton bidiyon ‘yan sanda dauke da manyan makamai na lakada wa Palasdinawa duka ya haddasa fusata a fadin yankin Gabas ta Tsakiya da sauransu, da suka hada da kasashen Larabawan da suka sasanta dangantakarsu da Isra’ila.
Harin rokoki da suka fada kan Isra’ila da kasar Lebanon, mai yiwuwa daga kungiyoyin Palasdinawa Ne, inda suka haddasa shiga mummunan hali mai cike da hadari a kan iyakar da aka girke makamai masu tarin yawa tun bayan da kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ta far wa Isra’ila a shekarar 2006.
A cikin kwanakin tun bayan wannan samame a al-Aqsa, duka bangarorin sun janye daga sake yin wani fito-na-fiton abubuwan fashewa, amma dalilan da suka sa suka kai ga wannan mataki har yanzu na nan.
Ya kai fiye da shekaru 10 tun bayan wani yunkurin da aka yi na saka Palasdinawa da Yahudawa su tattauna a kan makoma, ta zama tare ko kuma rabuwa. Lokutan da aka shafe na zaman rashin tabbas ya ja hankulan shugabannin Isra’ila musamman firaminista mafi dadewa a kan mulki, Benjamin Netanyahu, cewa za a iya sassauta tashin hankalin amma ba sasantawa ba.
Shekaru biyu na karuwar rashin jituwa da tashin hankalin tun bayan yakin Gaza sun yi nuni da yadda hakan ya zama akwai shakku a ciki.
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Tarayyar Turai da sauran su har yanzu na nanata amannarsu cewa dama daya kadai ta samun zaman lafiya ita ce samun bakin zaren warware matsalolin bangarorin biyu – samar da kasar Palasdinu mai cin gashin kan ta.
Wannan tsari ne na cewa kasar Palasdinu mai cin gashin kanta tare da Isra’ila zai bayar da dama ga duka bangarorin biyu su zauna lafiya da junansu.
Fadada matsugunan Yahudawa ba shi ne kadai dalilin da ya sa zaman sasantawa tsakanin Palasdinawa da Yahudawa ya gagara ba.
Amurka, wadda ta dauki nauyin zaman tattaunawar a baya, na da wata damuwar. Ta fi damuwa da gogayyarta da kasar China da kuma yakin da ke faruwa a Ukraine. Shugabancin siyasar Palasdinu ya samu rarrabuwar kai matuka tsakanin kungiyar Hamas a Gaza da hukumar Palasdinawa a gabar Yammacin Kogin Jordan.
Ba za su iya yin komai ba, idan aka duba yadda abubuwa suke, na yin wani katabus na yarjejeniya. Da matukar wahala Hukumar Palasdinawa ta iya yin wani katabus na amfani da wani karfin da take da shi.
Isra’ila na cikin nata matsalolin cikin gida na siyasa game da dimokradiyyarta.
Wanzuwar zaman lafiya tsakanin Palasdinawa da Yahudawa na da kamar wuya. Babu ko wane bangare da ya yarda da juna.
A cikin wannan shekarar wani mummunan tashin hankali da mace-mace babban gargadi ne na karuwar mafi munin tashin hankali nan gaba.
Kowa a nan ya san da hadarin da suke shiga. Babu wanda yake da wani ingantaccen tsari na shawo kan mummunan tashin hankalin da ke shirin kunnowa nan gaba.