• Skip to main content
  • Skip to primary sidebar
  • Skip to footer
  • Home
  • About Us
  • Contact Us

Americanahblog

American Immigration, Scholarships, News, Jobs And Marketing

Iran ta nada jakadanta a Saudiya bayan kasashen biyu sun daina gaba

22 September 2023 by Americanahblog

Spread the love


Iran ta nada jakadanta a Saudiya a daidai lokacin da kasashen biyu suka maido da hulda a tsakaninsu bayan sun shafe fiye da shekaru bakwai suna takun-saka.
Sabon jakadan, Alireza Enayati ya taba zama jakadan Iran a Kuwait, sannan ya rike mukamin mataimakin Ministan Harkokin Wajen kasar, yayin da kuma ya kasance darekta janar mai kula da lamuran kasashen yankin Gulf a Ma’aikatar Harkokin Wajen.
Saudiya da Iran da ke zama kasashe mafiya karfi a yankin Gabas ta Tsakiya sun rattaba hannu cikin ban-mamaki kan wata yarjejeniyar maido da hulda a ranar 10 ga watan Maris da ya gabata a kasar China.
Huldar da suka maido da ita bayan shafe tsawon shekaru ba-sa-ga-majiji da juna.
A shekarar 2016, Saudiya ta katse dangantaka da Iran bayan wasu masu zanga-zanga sun kaddamar da farmaki kan ofishin jakadancinta a Tehran da wani karamin ofishinta a Mashhad saboda hukuncin kisan da Saudiyar  ta zartas kan wani malamin Shi’a Nimr al-Nimr.
Gabanin gwamnatocin kasashen biyu su rattaba hannu, sai da suka gudanar da jerin tattaunawa a Iraqi da Oman.
Kafin dinke wannan barakar, kasashen biyu sun mara baya ga bangarorin da ke yaki da juna a yankin Gabas ta Tsakiya a tsawon shekaru, inda a Yemen, Saudiya ta goyi bayan gwamnatin kasar, yayin da Iran ta mara wa ‘yan tawayen Huthi.
RFI Hausa 

Related Posts:

  • Tarihin Rikicin Isra'ila da Falasdinawa Daga shekaru 100 Da Suka Wuce.
    Tarihin Rikicin Isra'ila da Falasdinawa Daga shekaru 100 Da…
  • Abinda Ya Jawo Yaki A Kasar Sudan Yanzu Haka.
    Abinda Ya Jawo Yaki A Kasar Sudan Yanzu Haka.
  • Yadda Amurka ta yi kokarin amfani da nukiliya wajen tarwatsa wata
    Yadda Amurka ta yi kokarin amfani da nukiliya wajen tarwatsa…
  • 'Yadda El-Rufai Ya Rushe Gidan Marayun Da Ya Shekara Sama Da 54 Da Ginawa A Zariya'
    'Yadda El-Rufai Ya Rushe Gidan Marayun Da Ya Shekara Sama Da…

Filed Under: LABARI

Americanahblog

About Americanahblog

A dedicated blog that blends education and travel. This is a space that embraces the wonders of learning and the thrill of exploring new places.

Primary Sidebar

  • Facebook
  • GitHub
  • Instagram
  • Pinterest
  • Twitter
  • YouTube

Trending

Transitional Milk and Mature Milk

Treating Breast Pain

Warning Signs of Breastfeeding Problems

Weaning Your Baby

When Not To Wean

Footer

About Us

Welcome aboard our thrilling journey that marries the world of education with the excitement of travel! Our blog is your ultimate compass, guiding you through the realms of study and adventure abroad.

Recent

  • Simple math but can you solve it? Quadratic Chanllege
  • 3 Easy Steps to Fail Post UTME
  • Top 10 Canadian Universities for African Students to Study in Canada
  • See How to Get Loan from NPF Microfinance Bank
  • Emotional Issues and Potty Training Problems

Search

Copyright © 2023 · AmericanahBlog Home · About · Contact · Privacy