Daga Fatima Nuraddeen Dutsin-ma.
Harkan Musulunci a Najeriya Karkashin Sheikh Ibrahim Zakzaky ta maka Gwamnar Jihar Kaduna Mal. Ahmad Elrufa’i a Kotun Duniya Wato ICC.
Ita dai wannan kotun kotun kasa da kasa ne mai hukunta manyan laifuka, wadda ita ce kotun kasa da kasa ta dindindin da aka kafa domin bincike da kuma gurfanar da mutanen da ake zargi da aikata manyan laifukan da suka shafi kasashen duniya da suka hada da kisan kare dangi, laifuffukan cin zarafin bil adama, laifuffukan yaki, da kuma laifin wuce gona da iri.
Kotun ta ICC tana da hedkwata a birnin Hague na kasar Netherlands, kuma tana da hurumin hukunta laifukan da aka aikata a yankin jihohin da suka amince da yarjejeniyar Rome, da yarjejeniyar da ta kafa kotun ta ICC, ko kuma ‘yan kasar.