A safiyar yau Litinin ne akan hanyar Jos zuwa Bauchi wannan mota mai dauke da mutane shida ta samu hadari. Inda biyar daga cikin su Allah ya karbe rayuwa su (hudu mata namiji daya) sai direban da ya samu mummunan ciwo.
Kamar yada muka samu labarin dukkanin su ‘yan uwa daya ne da suke da zama a cikin garin Jos anguwar Rogo.
Hadarin dai ya faru ne sanadiyyar wani kare da ya ketaro kan hanya, inda a kokarin kaucewa karen ne mota ta kwace har ta dake falwaya dake a gefen hanya.