Iran ta nada jakadanta a Saudiya a daidai lokacin da kasashen biyu suka maido da hulda a tsakaninsu bayan sun shafe fiye da shekaru bakwai suna takun-saka.
Sabon jakadan, Alireza Enayati ya taba zama jakadan Iran a Kuwait, sannan ya rike mukamin mataimakin Ministan Harkokin Wajen kasar, yayin da kuma ya kasance darekta janar mai kula da lamuran kasashen yankin Gulf a Ma’aikatar Harkokin Wajen.
Saudiya da Iran da ke zama kasashe mafiya karfi a yankin Gabas ta Tsakiya sun rattaba hannu cikin ban-mamaki kan wata yarjejeniyar maido da hulda a ranar 10 ga watan Maris da ya gabata a kasar China.
Huldar da suka maido da ita bayan shafe tsawon shekaru ba-sa-ga-majiji da juna.
A shekarar 2016, Saudiya ta katse dangantaka da Iran bayan wasu masu zanga-zanga sun kaddamar da farmaki kan ofishin jakadancinta a Tehran da wani karamin ofishinta a Mashhad saboda hukuncin kisan da Saudiyar ta zartas kan wani malamin Shi’a Nimr al-Nimr.
Gabanin gwamnatocin kasashen biyu su rattaba hannu, sai da suka gudanar da jerin tattaunawa a Iraqi da Oman.
Kafin dinke wannan barakar, kasashen biyu sun mara baya ga bangarorin da ke yaki da juna a yankin Gabas ta Tsakiya a tsawon shekaru, inda a Yemen, Saudiya ta goyi bayan gwamnatin kasar, yayin da Iran ta mara wa ‘yan tawayen Huthi.
RFI Hausa