Hukumar INEC ta dakatar da kwamishinan zaɓe na jihar Adamawa, Barrister Hudu Ari daga Aiki. Nan take. Hudu Yunusa Ari Dan jihar Bauchi ne daga karamar hukumar Ningi.
Cikin wata sanarwa da ta fitar yau Litinin, INEC ta umarci kwamishinan ya fice daga ofishinta har sai abin abin da hali ya yi.
Sakamakon gaggawan sanar da Sakamakon zaben Gomnan jihar Adamawa da yayi ba bisa cika ka’ida ba.
Ta ce daga yanzu sakataren hukumar a jihar Adamawa ne zai karɓi ragamar aiki.
Jami’ar hukumar zaɓen Zainab Aminu Abubakar, ta ce an dakatar da kwamishinan zaɓen ne har sai an kammala bincike, inda daga nan ne INEC za ta bayyana matsayarta kan lamarin.
A ranar Lahadi ne kwamishinan zaɓen Adamawa ya fito ya sanar da Aisha Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen gwamnan jihar tun kafin a kammala tattara sakamako.
Wanda hakan ya so haifar da rudani a jihar.
Sai dai INEC ta ce matakin da ya ɗauka haramtacce ne, don haka ba za a yi aiki da shi ba. Sai an kammala bincike. Kan zaben.