Shugaban Ƙasa Muhammadu mai barin gado, Muhammadu Buhari ya nemi afuwar al’ummar ƙasar game da wasu manufofin gwamnatinsa waɗanda ya ce ya san sun haifar da damuwa tsakanin al’umma.
Shugaban ya fadi haka ne a jawabin da ya yi wa al’ummar kasar, karo na karshe a matsayin shugaban kasa a yau Lahadi.
A lokacin da ya ke bayani kan tattalin arziki, shugaba Buhari ya ce “Tattalin arizikinmu (Najeriya) ya kara zamantowa mai jurewa saboda irin matakan da aka dauka domin ganin cewa bai durkushe ba a lokacin da tattalin arzikin duniya ya shiga mummunan hali.”
Ya kara da cewa “A kokarin inganta tattalin arzikin mun dauki matakai masu matukar wahala wadanda yawancinsu suka samar da sakamako mai kyau.”
“Wasu daga cikin matakan sun haifar da wahalhalu, kuma ina mai neman afuwar al’ummar kasa game da hakan. Sai dai mun dauki matakan ne domin amfanin wannan kasa.”
Ya kuma ƙara da cewa, “ina da tabbacin cewa zan bar Nijeriya a yanayi mai kyau sama da yadda na sake ta a 2015,”