Gwamnatin Jihar Kano ta ce daga yanzu kwacen waya ya zama daidai da fashi-da-makami a Jihar.
Hakazalika duk wanda aka kama hukunci iri daya za a rika yanke masa da dan fashi-da-makami.
Kwamishinan Yada Labarai da Al’amuran Cikin Gida na Jihar mai barin gado, Malam Muhammad Garba ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi.
Ya ce daukar matakin ya biyo bayan taron Majalisar Tsaro ta Jihar a zamantan na bankwana, wanfs Gwamna mai barin gado, Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranta.
A cewarsa, yawan faruwar kwacen waya a jihar a ’yan kwanakin nan abin damuwa ne wanda kuma ake bukatar tsatstsauran mataki kafin a iya dakile shi.
Ya kuma bayyana cewa tuni a ka fara shirin ɓullo da hanyoyi da za a magance ta’adar ƙwacen waya baki daya a jihar.