Majalisar kansilolin karamar hukumar Malumfashi a jihar Katsina, ta sanar da tsige mataimakin shugaban karamar hukumar Hon Abdulrazak Tukur Maifada daga mukaminsa.
Kazalika, majalisar ta kuma tsige jagoran majalisar kansilolin karamar hukumar, Hon Abdullahi Rabi’u, kansila daga mazabar Yaba daga mukaminsa. Dukkansu bisa zargin aikata wasu laifuka.
Sanarwar da Hon Salmanu Saminu kansila mai wakiltar mazabar Ruwan Sanyi ya karanta, ya bayyana kansa a matsayin sabon shugaban majalisar kansilolin. Sannan sun umurci mataimakin shugaban karamar hukumar da suka ce sun tsige da ya gaggauta kwashe kayansa daga ofishin cikin sa’o’i 24.
DCL Hausa ta ba da labarin cewa a shekarar bara 2022 ne dai aka gudanar da zaben ciyamomi da kansiloli a fadin jihar Katsina, bayan shafe shekaru kusan 6 ana tafka shari’a da wadanda gwamnatin Masari ta gada daga gwamnatin Ibrahim Shema, ta kuma sallame su daga aiki.
Ita ma dai APC a wancan lokacin, zaben da ta gudanar ya zo da wani abu da masana ke kira ‘shubuha’, inda ba a ga shugaban hukumar zabe ta jiha da ke da alhakin ayyana sakamakon zaben ba a yayin sanar da shi. Sai dai kwatsam, aka ga sakataren hukumar na zayyano sunayen wadanda aka ce sun yi nasara.