Daga: Comr Abba Sani Pantami
Akwai yiwuwar Litar man fetur guda takai 800 a gidajen mai na Gwamnati.
A jiya Litinin sabon shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu ya sanar da batun cire tallafin man fetur, kamar yadda ya fada tun a lokacin da yake yakin neman zabe.
Duk da kasancewar Najeriya na da arzikin man fetur, kasar ta kasa tace danyen manta domin biyan bukatun kasa, don haka take shigo da albarkatun man fetur wadanda kuma ake sayarwa kan farashin da Gwamnati ta kayyade. Kasancewar akasari farashin yana kasa da farashin da ake shigo da shi, sai Gwamnati ta rika biyan tallafin.
Amma tallafin yana shafar harkokin kudi na Gwamnati a shekarar da ta gabata, Gwamnatin ta kashe Naira triliyan 4.3 kwatankwacin dala 9.3 kan tallafin mai sannan cikin wata shida na wannan shekara, an ware Naira Tiriliyan 3.36 domin wannan bangare.
Kudaden da ake biya na shafar ayyukan gina al’umma kamar makarantu da asibitoci amma cire tallafin ba zai zo da sauki ba saboda zai janyo hauhawar farashin kayayyaki, talakawan kasa za susha wahala sosai.
A shekarar da ta gabata BBC Hausa tayi hira da shugaban kamfanin NNPC Mele Kyari idan ya tabbatar da cewa matukar Gwamnatin kasar ta cire tallafin Man Fetur to tabbas a Gwamnatance sai an koma saida kowace lita a matsayin kusan Naira 800, bamu san ya zata kasance a yanzu ba.
Sanadiyar cire tallafin Man Fetur zai jawo tsadar duk wani abu a Najeriya tun daga bangaren sufuri har zuwa kayan kamfanoni da na masarufi da sauran su.
Daga sanarwar da shugaban kasa ya bayar zuwa yanzu Allah ne kadai yasan iya gidajen Man Fetur din da suka rufe gidajen mai din su, sun dau aniyar boye Man Fetur din domin su samu riba mai yawan gaske da zaran dokar cire tallafin ta fara aiki, kuma idan ba’a yi da gaske ba za’a sha wahalar Man Fetur a cikin ‘yan kwanakin nan.
Na tabbata cire tallafin Man Fetur zai taimakawa Gwamnatin kasar wurin samun kudi sosai, amma talakawan kasar kowa zaisha wahala fiye da yadda ake tunani, duk yadda wasu suke zagin Gwamnan baya da ikirarin cewa Gwamnatin lalatacciyar Gwamnati ce ba karamin kokari ta yi ba akan batun tallafin Man Fetur ba, Buhari yaki ya cire tallafin ne domin yasan talakawane za sufi kowa shan wahala.
✍️ Comr Abba Sani Pantami