Majalisar wakilai ta Najeriya ce ta fara amincewa da dokar kafin ta kai gaban shubaban, inda ya rattaɓa mata hannu.
Dokar dai na neman samar da tsarin ilimi mai kyau da bunkasa fasahar koyon sana’o’i da kuma rage talauci tsakanin almajirai a Najeriya.
Har ila yau, dokar za ta kuma kyautata karatun sangaya da rayuwar almajirai da sauran yaran da ke gara-ramba ba su zuwa makaranta.