Ansake tura murja kunya tare dawasu mutane uku gidan gyaran hali
Ansake tura murja kunya tare dawasu mutane uku gidan gyaran hali

YANZU YANZU: Kotu ta sake tura Murja Kunya da Real Idris Mai Wushirya, Aminu BBC da Sadiq Mai Waƙar A daidaita nan zuwa gidan yari.
Kotu ta sake turawa da fitacciyar yar TikTok ɗin nan Murja Ibrahim Kunya da ƙarin wasu muatanen zuwa gidan gyaran hali.
Ya haɗada Babban abokin Murjan wato Ashir Idris wanda aka fi sani da Mai Wushirya sai kuma Aminu BBC da Sadiq Shehu Shariff wanda ya yi waƙar nan mai taken “A daidai ta nan”.
Zauren Malaman Kano ne ya yi ƙarar matasan bisa zargin wallafa bidiyoyin lalata tarbiyya atsakanin al’umma a dandalin TikTok.
Ana tuhumar Murja da Real Ashir Idris da yin bidiyon batsa a TikTok, inda ya amsa laifinsa yayin da ita kuma ta musanta.
An kuma tuhumi Aminu BBC da yin bidiyon batsa a dandalin TikTok wanda ya musanta.
Sai kuma Sadiq Shehu Shariff mai waƙar “A daidai ta nan” wanda aka zarga da yin waƙar batsa zargin da ya musanta.
A nan ne lauyoyinsu suka nemi a basu belinsu, sai dai lauyan Gwamnati yaki yadda dahakan, inda ya nemi a basu mako guda domin su yi martani.
Kotun ta tura su zuwa gidan yari har zuwa 23 ga watan Fabrairun da muke ciki.
Dangane da tuhumar da aka soma yiwa Murja a zaman da ya gabata kuwa, Murja ta rubuto takardar cewa ta tuba, inda Kotun ta ce za ta yi nazari a zama na gaba.