Daga: Sheikh Yakub Yahaya Katsina a Shekarun baya.
Wani lokaci mun je Umra da Sayyid Zakzaky (H) a Saudiyya, sai muka je Uhud (Inda aka yi yaƙin Uhud) sai Malam ya fiddo mafatihu yana karantawa, sai wani ya zagayo ta bayan Malam ya sako hannunsa ya zare littafin, to sai Malam ya juyo ya ce masa bani littafin akwai abin da zan ɗauka a ciki. Malam ya amsa ya zari wata takarda, sai ya miƙa masa littafin.
Abin da yasa Malam ya yi haka, saboda akwai wani lokaci da suka taɓa yi masa haka, suka amshi mafatihun, to sai suka ga sunansa a jikin littafin da kuma adireshinsa. To an sami matsala a lokacin. Shi ne a wanann karon sai ya zamana Malam yaƙi rubuta sunansa a jiki.
To amma ita waccan takardar da ya amsa akwai sunansa a jiki da kuma adreshinsa, shi yasa ya yi hakan.
Bayan mun dawo sai ni suka ganni da mafatihu, sai ga ma’aikatan nan sai suka kamani suka yi mani tambayoyi da larabci naƙi basu amsa, sukayi da farisanci, sukayi da yarurruka nayi shiru na kyale su. To sai Suka hau dani can saman bene. Office din da suka kaini yafi girman wajen nan da muke ciki.
Babban waje ne. Sai suka kai ni wajen wani mutum mai geme sosai. Sai ya tambaye Ni mi nake yi da wannan littafin. Sai nace ai wannan littafin addini ne, addu’o’i kawai ne a ciki. To sai yace man “wanann littafin haramun ne a riƙa karanta shi, haramun ne” to sai ya ɗauko wasu littattafai na izala ya bani.
Bayan na fito sai nazo wajen su Malam na ba su labari. Sai Malam yake dariya ya ce min ai sun kwace maka zinaren sun baka karfe”.
Hmmm! Yanzu ko Makka ma ba ta zuwuwa. Ba ya yiwuwa mu sake zuwa Makka, yanzu sun kashe mutum. Don rabonmu da Makka tun shekarar da aka haifi su Hassan.
Saboda akwai zuwan da mukayi suka kama Malam (H). Bayan mun gama Umra mun gama bankwana munyi ziyara, har mun gama haɗa kaya mun fito muna shirin shiga Mota. To zirga-zirgar da muka yi ashe sun lura da Malam. Sai suka kama shi suka tafi da shi.
To muna nan muna jira, haka dai cikin ikon Allah sun je sun yi abin da suka yi suka sake shi.