Daga: Aliiy Usman Nayara
Majalisar dokokin Iran ta kori ministan masana’antun ƙasar sakamakon hauhawar farashin kayayyaki.
Reza Fatemi ya gaza samun goyon bayan da yake buƙata domin tsallake matakin majalisar.
A shekarar da ta gabata ne, Jagoran addini a Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya soki matsalar tashin farashin kayayyaki da kuma rashin ingancin kayayyakin da ake sarrafawa a ƙasar.
Tattalin arzikin Iran na fuskantar ƙalubale sakamakon takunkuman da ƙasashen yamma suka ƙaƙaba saboda matakin gwamnati na ci gaba da tafiyar da shirinta na nukilya.
Matakin ya sa ana ta samun hauhawar farashin kaya da kuma karyewar darajar kuɗin ƙasar a kan dala.