Daga Anas Saminu Ja’en
Rundunar ƴan sandan jihar Kano sun yi Holen mutum 44 ƴan ta’addan da ake zargin su da laifuka iri-iri a sassan daban-daban, Kuma a cikin su masu ƙashe mutum ko raunata shi su ƙwace wayar sa a jihar Kano.
Kuma Kakakin ƴan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa bayan ya wallafa a shafin sa na Facebook, ya ce rundunar ta umarci al’umma da su duba hotunan nan da kyau ko za su gane wani a cikin su, ko ya taɓa yi muku sata a baya ku kira wannan lambar 0803 278 5908.