DAGA: Abdul-Hadee Isah Ibraheem.
A goman ‘karshe na watan Ramadan Yaki me muni ya balle a kasar Sudan (Sudan Ta Arewa) wanda yayi sanadin kashe mutane sama da 800 zuwa yanzu, abubuwan da suke faruwa a Sudan a yanzu ba lallai ne ka iya jin hakikanin su a manyan kafafen watsa labarai na duniya ba.
~ Yakin yana faruwa ne tsakanin Sojojin gwamnatin kasar (Military) wanda shugaba Abdul Fattah Al-Burhan yake jagoranta, da kuma bangaren ‘yan Awaren da suka balle daga Sojojin kasar da wasu hadaddun Kungiyoyin tsaro (Para military) da ake kira da “Rapid Support Force” ko (RSF) karkashin jagorancin General Muhammad Hamdan, wanda yana daga cikin manyan masu kudin kasar duk da cewa Soja ne, shine yake da babban Kamfanin Al-Junaid.
~ Me ya jawo yakin?
Bari mu dauko batun daga asali.
Babban abinda ya jawo yakin yana da asali ne tun daga 1993 lokacin da tsohon shugaban kasar Umar Hassan Al-Bashir ya karbi Mulkin kasar, yadda ya shugabanci kasar da yadda mu’amalar sa ta kasance me ‘daci tsakanin Sudan da kasashen Turawan Yamma. Musamman kashe kashen da ya faru a Daffur a wajejen 2003 zuwa 2005.
~ Wanda daga baya a 2009 ICC wato Kotun Hukunta manyan laifuka (International Criminal Court of Justice) ta nemi a kamo mata Al-Bashir. Ya bijirewa kasashen yammacin duniya sosai, kuma basu ji dadi yadda Albashin ya rike kasar sa ba.
~ Daga karshe America da England sukai ta kakabawa Sudan Takunkumin tattalin arzikin (Economic Sanctions) na tsawon shekaru har zuwa yau, da kyar Sudan take motsawa duk da cewa itace kasa ta Uku mafi girma a Africa.
~ Bayan Al-Bashir ya bar Mulki ranar 11 ga watan April 2019 wadanda suka hau Mulki a bayan sa sun fahimci cewa kasar ba za’a iya mulkin ta da sauki ba a wannan yanayin na Takunkumin tattalin arzikin, dole suka nemi gudummuwar kasashen Africa, babu wata kasa data taimake ta sai Nijar da Eritrea.
~ Takunkumin yayi matukan kassara mutanen kasar, sun ji jiki sosai har yau suna jin jiki, Sudan itace kasa ta Goma a duniya da suka fi kowa yawan Arzikin Gold🥇, amma babu inda zasu kai su siyar a hukumance saboda suna karkashin Takunkumi.
~ Kuma ba za’a siyar mata ba, ba zata saya ba, kasar ta rushe sosai Economically gaskiya, bayan wucewar Al-Bashir ne ‘yan kasar suka fara jinjina masa da yin kewar ina ma ace ya dawo.
~ Sudan tana da Arzikin Man Fetir sosai bayan Zinare, Sudan tana fitar da Na’ukan Crude Oil har guda uku ita kadan ta. Daga watan January zuwa June na 2020 Sudan ta fitar da Man Fetir da kudin sa ya hau Dala Miliyan $317. Amma duk da haka kudin baya amfanar kasar koda da kaso 10 cikin 100 saboda sanctions din da suke kai.
~ Kasashen Africa basu nuna tausayawa Sudan balle su taya su rage radadin halin da suke ciki. Don haka Sudan taga cewa idan ta cigaba da yin shiru bata nemi taimakon wasu kasashen duniya ba toh gaskiya nan gaba za’a wayi gari babu kasar.
~ Domin neman mafita daga halin da take ciki (Sudan) da kuma tayar da tattalin arzikin kasar ta sai Sudan taga cewa dole fa ta hada kai da manyan kasashen duniya da suke da arziki kuma suke fada da America irin su Rasha, China da India, don su taimaka mata wajen farfado da arzikin ta, kuma su jawo kasashen da suke da iko dasu su shiga Huldar kasuwanci da Sudan.
~ Nan take Rasha tazo Sudan a watan January na 2022 ta tattauna da jami’an kasar tare da cimma yarjejeniya guda hudu kamar haka:
1. Rasha tace zata zo ta kafa Cibiyar tsaron Sojojin ruwan ta (Navy) akan Ruwan Kogin Red Sea dake Arewa da Sudan wanda yana daga cikin wuraren da Sudan take da iko dasu.
2. Na biyu, Rasha zata Aiko da Sojoji guda Dari uku domin bayar da kariya wa Sudan daga Makiyan ta, na tsawon shekaru 25 tare da ‘karin shekaru 10 idan wadannan shekaru 25 sun kare ba’a Kai ga cimma abinda ake so ba.
3. Na uku, Rasha zata zo da Makamai masu linzami kan ruwan Maliya (Red Sea).
4. Rasha zata sayi Man Fetir da Gold daga Sudan, da kuma jawo kawayen ta suzo su saya daga Sudan din suma.
~ Toh daga jin wannan matsayar da Sudan ta cimma da Rasha sai America tayi magana ta bakin Sakataren Gwamnatin kasar Antorney Blinken, tana gargadin Sudan kada ta kuskura tasa hannu akan wadannan yarjejeniya. Sudan taki ji domin daga baya tasa hannu.
~ Wannan ne dalilin da yasa America ta shiga kasar ta raba kan jami’an tsaron kasar, tare da karfafa Sojojin da suka balle daga gwamnati wato (RSF) na General Muhammad Hamdan, suyi yaki domin a kawar da gwamnatin Abdul Fattah Al-Burhan.
~ Kasancewar US tana da boyayyun makamai a Libya, wadanda suka bayar wa Gaddafi amma yaki yin abinda US take so, aka kawar dashi, kuma aka samu Access da inda Makaman suke, don haka America bata da matsalan makamai idan za tayi yaki a Africa, balle kasar Sudan da take kusa da Libya.
~ Dan haka US tana tare da Para military na RSF ita kuma Rasha tana tare da gwamnatin kasar ta Sojoji, ana buga yakin ne a Khartoum babban birnin kasar, wanda ake ganin zai watsu zuwa sauran sassan kasar irin su Dafur.
~ RSF suna yaki ne a madadin Sojoji America, tare da samun support daga US din. Bisa alkawarin idan sunyi nasarar kifar da gwamnatin Abdul Fattah Al-Burhan su zasu rike kasar.
~ Sai dai asali tun farko ita Rasha bata so a kai ga yaki ba, domin ta aiko da Sakataren ta ya zauna da bangarori biyun, idan sun yarda su mika mulki ga farar Hula daga baya zata zauna dasu. Rasha ta basu shawara su fara tsare kasar su tukuna, daga baya ayi maganar Diplomasiyya.
~ America da kawayen ta sai suka zuga bangaren Muhammad Hamdan cewa kar su amince, a buga yaki kawai me karfi ya karbi Mulkin.
~ Ina ganin zan tsaya a nan, amma a rubutu na biyu zamu kawo sauran bayanan, musamman:
1. Shin babu yaudara a alkawuran da Rasha tayi wa Sudan?
2. Su wa ake nufi da wannan yakin bayan Sudan?
Allah yasa mu dace, ya zaunar damu lafiya, ‘yan uwan mu ‘dalibai da suke Sudan Allah ya kubutar dasu, ya tsare su, da dukkan Musulmi da suke can din.