Daga: Zuhair Ali Ibrahim Zariya.
A jiya Juma’a 14/4//2023 ne Ƴan shi’a mabiya Sheikh Zakzaky na duk Najeriya da maƙwafta kamar su Nijar da dai sauransu maza da mata manya da yara su ka fito Zanga-zangar lumana domin barranta da irin zaluncin da Isra’ila ke yi akan al’ummar kasar Palastinu, sannan tare da jaddada cewa; Masallacin Quds ta Musulmi ce.
Ƴan shi’ar dai sun fara wannan Zagayen ne bayan idar da Sallah juma’a kamar yadda suka sabayi a duk shekara, wasu kuma sun fara da Safiyace tun kafin lokacin Sallan.
Sai dai a wasu garuruwan a nan gida Nijeriya zanga-zangar ya bar baya da kura, kamar Abuja, Kaduna, inda Jami’an tsaron Najeriya suka kawo cikas, biyo bayan bude wuta da sukayi akan wasu mambobin na mabiya mazhabin Shi’ar, tare da rasa rai na Mutum daya da jikkata wasu da Daman Gaskiya.