Mai POS yaji Alert din miliyan 280 bai tambayi Dalili ba kawai Sai ya zamo attajiri har ya Fara tura mutane aikin Umara ya kuma sayi Gidaje jiya kuma magana ya tashi a Sai kudin………
An kama wani mai Sana’ar tura kudi ta ( POS) da aka bayyana da suna Alfa Rafiu a jihar Kwara kan zargin kashe naira miliyan 280 da aka tura asusunsa bisa kuskure,
Jaridar Nigerian Tribune ta habarto cewa . wanda ake zargin mazaunin Akuji da ke yankin Abayawo a karamar hukumar Ilorin ta yammacin jihar.
Angano mai POS “Yana Ta Kashe Kudi Son Ransa”: An Turawa Mai POS Miliyan N280 Bisa Kuskure, kawai shi kuma ya kama Kashe Su
Cikin gaggawa da zafin Nama lokaci guda ya tura kudaden cikin wasu Asusu kuma ya sayi Gidaje biyu masu kyau ya kuma sayi motar Hawa mai tsada ya tura wasu makusantan sa Umara suyi masa adduoi yanzu haka ma suna can basu dawo ba hukuma kuma ta kama shi.
Banki ne bisa kuskure suka tura miliyan 280 wanda bai da masaniyar komai a kansa. “Sai dai maimakon ya ja hankalin bankin da ya tura masa wannan makudan kudin bisa kuskure, sai ya hau kashe su cikin sauri.
“Rafiu ya siya gidaje, motoci sannan ya tura mutane Umrah. Wasu daga cikin wadanda ya dauki nauyinsu suna Saudiyya a yanzu haka da muke magana.
Sannan ya cigaba da yi wa“ wa mutane da dama alkhairi a garin, ya kuma Raba abinci Azumi da tufafi ga mutane masu yawa ya saya ma wasu abokan sa babura. Lokaci guda ya zamo Dan karamin Sarki Kowa neman sa yake yi har an fara Kiran sa Alhaji Sa’a.
Amma wasu mazauna unguwar su sun razana da irin abin da yake yi har ya kai ga sun janyo hankalin Jami’an tsaro. Domin kuwa suna ganin yanda akayi yayi kudi farat daya a matsayinsa na mai POS.” Akwai abun zargi a ciki. Kuma shi Bai fadi komi ba game da Sabon Arziki da yazo masa kawai sha’anin gaban sa yake yi babu dare babu Rana daga Alheri Sai sayan Gaddara da kayan Sawa iri iri wanda hakan yasa mutane shakka suka ja hankalin hukuma kan sa.
Tun kafin hakan ma asai bankin sun ankare sunyi kuskure har sun fara neman sa ruwa a jallo.
An tattaro cewa yan sanda daga ofishin “C” Division da ke Oja-Oba, Ilorin sun kama wanda ake zargin da rakiyar wasu jami’an banki.
Da jaridar Daily Trust ta ziyarci yankin nasa a ranar Talata, shagon POS dinsa ya kasance a rufe sannan wasu mazauna gidan sun ce ya yi tafiya basu san yaushe zai dawo ba.
Kakakin yan sandan jihar Kwara, Ajayi Okasanki ya tabbatar da lamarin. “Eh, da gaske ne, amma sashin FCIID daga Alagbon-Close, Ikoyi, Lagas ne suka aiwatar da kamun nasa wanda hakan ya fita daga hannunmu.”
Wai in Kaine ka samu wannan Damar zaka Tuntubi Bankin ne ko kaima zaka fantama kawai….?