Ko’odinetan kungiyar kamfen din Tinubu/Shettima na Bayelsa, ICC, Prince Preye Aganaba, ya ce masu sukar shugaban kasa mai jiran gado, Sen. Ahmed Bola Tinubu, za su zama na farko-farko a masu yabon sa bayan ranar 29 ga watan Mayu.
Aganaba, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Yenagoa, ya ce galibin mutanen da ke sukar Tinubu, na yi ne da jahilci, yayin da wasu da su ka san shi amma su ka zabi su ƙi shi, suna yin hakan ne saboda hassada.
Aganaba, wanda ya taya ƴan APC murnar dawowar zababben shugaban kasar daga kasar Faransa, ya ce masu ƙin Tinubu bisa taurin kai za su dawo su na yabon sa, yayin da manyan makiyansa za su binne kawunansu cikin kasa saboda kunya bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu.
Ya bayyana kwarin guiwar cewa Mista Tinubu zai bata wa makiyansa rai a kan ayyukansa, inda ya kara da cewa tsohon gwamnan jihar Legas ɗin ya yi fice wajen kwazon aiki.