Iyayen daliban Najeriya da aka kwashe a Sudan zuwa kasar Masar sun ce direbobi sun kara watsar da su a cikin sahara bisa umarnin kamfanin jigilar da ya kwaso su.
Iyayen Rukunin farko na daliban da suka bar birnin Khartoum na Sudan a ranar Laraba sun koka cewa yanzu kwana uku amma har yanzu ’ya’yan nasu ba su shiga kasar Masar ba.
Sun bayyana cewa a cikin ayarin har da iyalai da kananan ’ya’yan ’yan Najeriya mazauna Sudan, amma babu wani tanadi da aka yi musu na abinci ko ruwa ko wurin fakewa, a tafiyar ta awa 18 daga Khartoum zuwa iyakar kasar Masar.
Wani daga cikin iyayen da ya ce ’ya’yansa biyu na daga cikin ayarin farko na motocin da suka dauko ’yan Najeriya daga Khartoum ya ce karo na biyu ke nan da kamfanin jigilar yake watsar da ’ya’yan nasu a tsakiyar sahara, a iyakar Sudan da Masar.