TASKAR LABARAI

Wani Alkalin kotu Yasha Duka a Hannun Wasu Ma’aikata a Jihar Kebi

Wani Alkalin kotu Yasha Duka a Hannun Wasu Ma'aikata a Jihar Kebi

Birnin-Kebbi: Wata kotun majastiri dake zamanta a baban birnin Jihar kebbi, Birnin-kebbi, ta gabatar da wani babban darakta a hukumar ilimin mai ta jihar, Aliyu Shehu jega da wasu mutum biyu kan zargin dukan Alkalin kotu.

Wandanda dai ake zargin sun bayyana a gaban kuliya, su uku domin amsa laifin hada baki, tare da dukkan ma’aikacin kotu.

Yayin da mai gabatar da kara ke bayani yace “wanda ake zargin, yan sanda ne suka kama su tare da gurfanar da su a gaban kotu kan dukan Alkalin kotun majastirin.

Mai gabatar da kara Dan Sanda Jubril Abba yace suna bukatar kotu ta basu dama dan ganin sun kara kimtsawa tare da gabatar da shedu a gabanta kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Mai shigar da karar yace ana zargin masu laifin ne da hukuncin sabawa doka, taka hukuncin kotu da kuma laifin cin zarafi

Yace abinda ya faru shine:

lokacin da alkalin kotun yaje babbar ma’aikatar ilimi ta jiha a birnin kebbi, ya je zai yi alwala sai aka samu sabani da shi da daraktan wanda ta janyo ce-ce kuce wanda daga bisani ta sa daraktan marinsa baya da wasu mutum biyu da suka tayashi wajen dukansa.
Yace wanda aka daka din yana matakin na 16 na a aikin gwamnati, kuma shine Alkalin kotun majastiri mai mataki ta uku, indai za’ai masa haka to ina muka dosa.

Yace wannan ne shine lokaci na farko da aka taba ji ko gani yadda aka daki wani Alkalin kotu. kuma a kwanan ma ga yadda aka kashe wani alkali a gidansa. Ina ake so wannan abun ya tsaya?

Bayan ji ta bakin wanda suka shigar da karar Mai-Shari’a Hassan Kwaidijo ya daga shari’ar zuwa 28 ga watan nuwanban wannan shekarar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button