TASKAR LABARAI

Shugaba Buhari Zai Kaddamar Da Tonon Arzikin Man Fetur Na Farko A Arewa

Shugaba Buhari Zai Kaddamar Da Tonon Arzikin Man Fetur Na Farko A Arewa

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Talata zai jagoranci kaddamar da hakan arzikin man fetur na farko a tarihin Arewacin Najeriya.

Za’a fara hakan arzikin mai a jihar Bauchi da Gombe.

Wannan hakar arzikin mai da zai kasance a Kolmani (OPL) 809 da 810.

Shekaru biyu da suka gabata aka gani arzikin man fetur a Arewa. Gabanin gano arzikin, yankin Neja Delta kadai ke da arzikin man fetur a Najeriya.

Tun 2016, NNPC ta fara neman arzikin mai a wasu jihohin Najeriya kuma aka samu nasara a Bauchi, Gombe, Borno da Neja.

A cewar hukumomi a NNPC, kamfaonin da aka baiwa kwangilan hakan mai sun hada da Sterling Global Oil, New Nigeria Development Commission (NNDC) and NNPC Limited.

“Bikin fara tonon zai gudana ne ranar Talata, 22 ga watan Nuwamba kuma shugaban kasa da kansa zai halarta tare da yawancin ministocinsa fari da karamin Ministan man fetur, Timipre Sylva.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button