TASKAR LABARAI

Majalisar ɗinkin duniya ta bukaci a yi Hukunci kan kisanda Ɗan Sandan Da Ya Yiwa Lauya

Majalisar ɗinkin duniya ta bukaci a yi Hukunci kan kisanda Ɗan Sandan Da Ya Yiwa Lauya

Majalisar ɗinkin duniya ta bukaci a yi Hukunci kan kisanda Ɗan Sandan Da Ya Yiwa Lauya.

Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) a Najeriya ta yi Allah wadai da kisan wata ‘yar Najeriya, Misis Omobolanle Raheem, haka wata lauya a jihar Legas itama ta buƙaci a yi adalci kan wanda ya aikata wannan ɗanyen aiki.

Mai kula da ayyukan jin ƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya, Matthias Schmale a cikin wata sanarwa kwanan nan ya ce kisan ya kasance mai matuƙar tayar da hankali da baƙin ciki ko da ya ke miƙa ta’aziyya ga iyalan Misis Raheem, da kuma kwararrun aminan aikinta da abokanta.

Wani ɓangare na sanarwar ya ce “Muna roƙon da a gaggauta yin adalci ga Misis Raheem da danginta.

 

 

 

“Ina kuma ƙara ƙarfafa gwiwar gwamnatin Najeriya da ta sake duba tare da ƙarfafa aiwatar da ƙa’idojin aikin rundunar ‘yan sanda, da kuma ƙa’idojin aiki na ‘yancin ɗan adam, domin hana afkuwar irin wannan lamari a nan gaba.

“Kamar yadda wata shekara ke ƙarewa, abin damuwa ne cewa ba a la’akari da annobar cin zarafin mata da ‘yan mata ba. Majalisar Ɗinkin Duniya za ta ci gaba da baiwa gwamnatin Najeriya da ‘yan sandan Najeriya goyon baya wajen kare mata da ‘yan mata daga duk wani nau’i na cin zarafi da kuma tabbatar da cewa an mutunta ‘yancin ɗan Adam na masu rauni a cikin al’umma.”

 

RAHOTO DAGA:- Comrd Yusha’u Garba Shanga.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button