• Skip to main content
  • Skip to secondary menu
  • Skip to primary sidebar
  • Skip to footer

Americanahblog

American Immigration, Scholarships, News, Jobs And Marketing

  • Home
  • Info Hub
  • Scholarship
  • Education
  • Contact Us
    • Privacy Policy
    • About Us
    • Terms and Conditions

MACE A MAHANGAR ZAMANTAKEWA !

10 April 2023 by Americanahblog

Spread the love

 

MACE A MAHANGAR ZAMANTAKEWA ! 

A mafiya rinjayen tunanin mutanenmu ( hausawa) suna daukar mace a mahangar zamantakewa wata abace ta biyan bukata kadai, ba tare da duban tarin damarmakin da Allah ya bata ba.

Meyasa bama cire sha’awan da ke tsakaninmu ( mace da namiji) mu dora ita macen a mahangar zamantakewa da rayuwa na yau da kullum?. 

A cikin irin al’ummar da muke da su a kasata (Nigeria) hausawa na cikin kaso mafi rinjaye da suka mayar da mace kayan anfani da biyan bukata, bayan wannan mace batada wani anfani a wajensu, kadan daga cikin su ne ke zama da mace a matsayin abokiyar rayuwa. 

Shin ko kinsan cewa kece mutum na farko daya bayar da dama dari bisa dari na wanzar da wannan mummunan tunanin a tsakankanin al’umma ? .

Tun farko ke ce kike daukar kanki a matsayin wata abar sha’awa, birgewa da daukan hankali ga namiji, kika dauka banda biyawa miji bukatar sha’awarsa da yi masa sauran ayyukan gida baki da wani sauran anfani, taya shi kuma bazaya daukeki a yanda kike so a daukeki ba. Tabbas ke abar burgewa da sha’awa ce, Amma idan wannan burgewa din da sha’awan suka kare shikenan kin gama aiki kenan? Ansar itace A’a kuma eh ga wacce ta zabi hakan. Kinada damar kasancewa abokiyar zamantakewa ga mijinki ta hanyoyi da yawan gaske ba sai iya wa’yancan ba.  

Mace a mahangar zamantakewa ana bukatar ta zamana ko da so da kauna ya kare a tsakanin ta da mijinta to still akwai dalilin da zaya zaunar da ita gareshi , bawai ina nufin tunda ta haifi yara yanzu zamansu zatayi ba, a’a ko basu haifi kowa ba har suka shekara dari to dalilan kasancewarsu tare kullum suna nan. Ba its girki, haihuwa, raino, kwanciya kadai kike da tasiri ba. 

Anaso ne ki kasance a matsayin masoyiya, matar aure, abokiyar rayuwa, abokiyarsa, abokiyar sirrinsa, abokiyar shawararsa, abokiyar nemansa, abokiyar rufin asirinsa, abokiyar karatunsa, abokiyar namen aljannarsa, abokiyar kare mutuncinsa, abokiyar, abokiyar, abokiyar….

Kowane daya daga cikin wa’yannan abubuwan, ya zama idan kun rabu anan to zaku hadu acan, idan soyayyah ta kare to zaku cigaba da zama a matsayin abokai, idan abota ta kare zaku cigaba da zama a matsayin abokan rufin asiri, kowane daya ya kauce to ya zamana kunada wanda zaku tsaya akai. Bawai ki zamana kina tsufa kika fara gazawa da biya masa bukata da aikace-aikacen gida shikenan kin tashi aiki ba. A’a duk tsawon tafiya aje dake. Kece kike bada damar kasancewarki mace a mahangar zamantakewa ko kuma mace a matsayin abun biyan bukata, motsinki da aikinki su ne suke fassara hakan.

Amma yanada kyau ki gane cewan ba dan wannan kadai Allah yayo ki ba, kuma yanda Allah zaya tambayi namiji akan yanda ya gudanar da rayuwarsa, kema haka zaya tambayeki, dan haka sai ki tanadi ansar bayarwa tun kafin lokaci ya kure maki.

Shin kinyi abinda ya kamata kiyi ?

Kin rayuwa yanda ya kamata ?

Allah yasa mu dace

©️ Zarah A Zamsarf ✍🏽

Related Posts:

  • 1684660591435970-0.png
    Tarihin Rikicin Isra'ila da Falasdinawa Daga shekaru…
  • Abinda Ya Jawo Yaki A Kasar Sudan Yanzu Haka.
    Abinda Ya Jawo Yaki A Kasar Sudan Yanzu Haka.
  • 1685343325327969-0.png
    'Yadda El-Rufai Ya Rushe Gidan Marayun Da Ya Shekara…
  • 1684742079105636-0.png
    Yadda Amurka ta yi kokarin amfani da nukiliya wajen…

Filed Under: ZAMANTAKEWA

About Americanahblog

A dedicated blog that blends education and travel. This is a space that embraces the wonders of learning and the thrill of exploring new places.

Primary Sidebar

  • Facebook
  • GitHub
  • Instagram
  • Pinterest
  • Twitter
  • YouTube

Trending

PTDF Postgraduate Scholarship Scheme for Nigerians to Study Overseas

Petroleum Technology Development Fund, PTDF Postgraduate Scholarship Scheme for Nigerians to Study Overseas 2024/2025 (Study in UK, France, Germany, China and Malaysia)

Transitional Milk and Mature Milk

Treating Breast Pain

Warning Signs of Breastfeeding Problems

Weaning Your Baby

When Not To Wean

Footer

About Us

Welcome aboard our thrilling journey that marries the world of education with the excitement of travel! Our blog is your ultimate compass, guiding you through the realms of study and adventure abroad.

Recent

  • Adeyemi College of Education Ondo, ACEONDO Acceptance Fee Details for 2024/2025 Academic Session [NCE & Degree]
  • Nasarawa State University Keffi, NSUK Resumption Date for 2024/2025 Academic Session
  • Full List of Courses Offered In MAUTECH and their Cut Off Mark | Modibo Adama University Of Technology Courses
  • Bayero University Kano, BUK Part-Time Degree Admission Form 2024/2025
  • University of Benin, UNIBEN Academic Calendar for 2024/2025 Academic Session

Search

Copyright © 2025 · AmericanahBlog Home · About · Contact · Privacy