Jami’an hukumar kwastam, reshen filin jirgin saman Murtala Muhammed, MMA da ke Legas sun kwace fakitin tramadol 23 wanda kudinsa ya kai Naira biliyan 1.8 tsakanin watan Janairu zuwa Maris.
Kwanturolan hukumar, Mohammed Yusuf, a taron manema labarai a Legas a yau Laraba, ya ce an shigo da kayayyakin ƙwayoyin ne daga Indiya da Pakistan.
Yusuf ya lissafa kayayyakin da aka kama sun hada da fakiti 22 na tramadol (225mg) da fakiti 12 na tramadol (120mg).
A cewar Yusuf, an yi wannan kame ne bisa bayanan sirri da aka samu cikin filin jirgin saman.
Ya kara da cewa, hukumar ta shirya mika ƙwayar tramadol din da ke hannunsu ga kwamandan hukumar NDLEA da ke kula da filin jirgin Murtala Muhammed.
“ hadin gwiwa tsakanin hukumomin zai kara karfafa hadin gwiwarmu wajen kare matasanmu daga amfani da abubuwa masu cutarwa da ka iya jefa rayuwarsu cikin hadari da muhallinsu.
“Za mu kara himma wajen sanya al’ummominmu wuri mafi aminci ga dukkan domin samun zaman lafiya,” in ji shi.