Daga Abulfatahi Sani Attijani
Muna kira zuwaga Gwamnatin jihar Bauchi da Kano, cewa a ɗauki matakin gaggawa akan Wannan sakin baki da wasu daga cikin Malaman Kungiyar Izala sukayi akan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da sunan Tauhidi. Wanda Hakan yayi sanadiyyar Taɓa zukatan al’umma da dama Masoya Annabi Muhammaduﷺ a faɗin duniya.
Dalilin Wannan Sakin baki Hakika Allah ne kaɗai yasan iya Abinda zai faru, saboda haka muna kira zuwaga Gwamnatin jihar Kano da Bauchi Suyi Duba da irin Abinda Wannan lafuzan Zasu iya haifarwa a tsakanin Al’umma Da kuma Irin Abinda Wannan magana zata iya haifarwa na Fushi da fusata Ubangiji Ayi gaggawar ɗaukar matakan Hukunta wadannan Bayin Allah Tun Kafin Su sake janyo mana Wata Musibar Wacce Allah ne kaɗai yasan inda zata Tsaya.
Saboda haka Rayuwar mu ba abakin komai take ba, Indai Ana maganar Annabi Muhammadu ﷺ Kuma insha Allahu Sai inda Karfinmu ya ƙare Akan wannan mas’ala domin ba wurin da za’a taɓa bane muyi shiru.