Daga: Saliadeen Sicky
A Rana Mai Kamar Ta Yau 27 Ga Watan Mayu 1967 Gwamnatin Mulkinsa Soja Ta Janar Yakubu Gowon Ta Kirkiro Da Jihohi Guda 12 Ciki Harda Jihar Kano.
Kwamishinan Yansanda Audu Bako Shine Gwamnan Jihar Na Farko A Jihar.
Wannan jaha daga shekarar da aka ƙirƙire ta zuwa yau, ta samu jagorancin gwamnoni har goma sha shida daga shekarar haihuwarta 1967 zuwa 2015.
Kafuwar Jahar Kano.
Shugaban mulkin soja, Manjo-Janaral Yakubu Gowon, shi ya ƙirƙiri jahar Kano tare da sauran wasu jahohi goma sha ɗaya a Ranar 27 Ga Watan mayu na shekarar 1967.
Babbar manufar Shugaba Yakubu Gowon ta kafa waɗannan jahohi ita ce kusanta jama’a da gwamnati da kuma kusanto da gwamnati ga jama’a. Wato kenan ya zama jama’a sun je kusa da gwamnati ita ma kuma gwamnatin ta kusancin jama’a.
A ranar 5 ga watan Mayu, 1967 Shugaba Gowon ya wargaza yankuna hudu na ƙasar sannan ya ƙirƙiro Jihohi goma sha biyu (12). Jihohi shida sun kasance daga tsohon yankin arewa. Su ne: Jihar Arewa maso Yamma, Jihar Arewa maso Gabas, Jihar Kano, Jihar Arewa ta Tsakiya, Jihar Benue-Plateau da Jihar Kwara. Tsohon yankin yamma ya rabu zuwa Jihohi biyu: Jihar Yamma da Jihar Legas. Tsohon yankin tsakiyar yamma ya zama Jihar Yamma ta Tsakiya, yayin da tsohon yankin gabas ya dare zuwa Jihohi uku. Waɗannan su ne Jihar Gabas ta Tsakiya, Jihar Ribas da kuma Jihar Kudu-maso-Gabas.
Jahar Kano.
Bayan shekaru bakwai da samun ‘yancin kan Najeriya, wannan gari mai tarin albarka ya zama jaha, a cikin shekarar 1967.
Wannan jaha tana ɗaya daga cikin muhimman jahohin Najeriya, kuma kusan a yanzu ita ce cibiyar arewacin Najeriya ta fuskacin hada-hadar kasuwanci da siyasa. Ita ce jaha mafi yawan jama’a a duk faɗin Najeriya kamar yadda sakamakon ƙidayar jama’a da aka gudanar a 2005 ya tabbatar.