Kasar Iran Tayi Kira Ga Al’ummar Duniya Dasu Fito Gaba Dayansu Domin Nuna Goyon Baya Ga Al’ummar Palestine Da Masallacin Qudus
Hukumar Kasar Iran ta bayyana cewa; Yaumul qudus, wata rana ce da al’ummar musulmin duniya zasu domin nuna fushinsu akan zaluncin masu girman kai da ‘yan sahayoniyar duniya gaba daya.
Kiran yazo ne bayan kusan cikar wata daya ana azumin watan Ramadan da yin ibada.
Al’ummar musulmin duniya za su sake yunkurawa domin taimakawa al’ummar Palestine masu bayar da kariya ga alkiblar farko ta musulmai a matsayin amsa kiran Imam Khumaini(r.a) wanda yake kira da a yi gwagwarmaya da ‘yan sahayoniya da masu goyon bayan zaluncin duniya.