Kada Tinubu yayi jinkirin nada ministoci kamar yadda buhari yayi
Kada Tinubu yayi jinkirin nada ministoci kamar yadda buhari yayi

Bayan gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya , wanda Bola Ahmed Tinubu na jam’iyar APC ya yi nasarar zamowa sabon shugaban kasar, yanzu kuma hankali ya koma kan irin ƙalubalen da ke gaban sabon zaɓaɓɓen shugaban mai jiran gado.
Masana sun fara bayyana wasu jerin ƙalubale sake gabansa dayadda Tinubun zai magance, tare da kira gare shi da kada yayi wariya wajen yi wa Najeriya aiki.
BBC ta tattauna da Farfesa Tukur Abdulkadir, wani massanin kimiyar siyasa da ke jami’ar jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, wanda ya ce akwai buƙatar Tinubu ya fara aiki cikin gaggawa ba tare da ɓata lokaci ba kamar yadda buhari yayi abaya.
Kamar yadda a abubuwa suka faru a2015, kada ya sake ya maimaita abubuwan da Buhari ya yi a baya, kamar jinkiri wajen naɗa ministoci da shugabannin hukumomin gwanati.