Da Dumi- Dumi: Zazzafan Martanin Kasar Iran Ga Isra’ila A Kan Al’ummar Palestine, Duk Wata Barazana Da Isra’ila Zatayi Munyi Karfin Ta–Gwamnatin Iran.
Details: PressTv |
Martani daga kwamantan sojojin Iran General Musawi, inda ya yi watsi da cika bakin da wani babban sojan Israel na cewa za su iya kawo wa kasar ta Iran hari, yana mai jaddadawa Isra’ila ta yi kadan ta yi mana barazana akan soji.
Janar Abdurrahim ya kara da; Duk wannan maganar sunayi ne saboda su bai wa ‘yan sahayoniyar kasar karfin gwiiwa don su magance matsalar da suke fuskanta a cikin kasar su.
A wannan Larabar data gabata ne dai wani sojan Israel “Herzi Havel” ya bayyana cewa; A shirye muke mu kai wa kasar Iran hari, Ina ya kara da cewa Israel nada karfin da zata kai hari a kasashen kusa da kuma nesa da kasar ta.