TASKAR LABARAI

Bidiyan matashin daya tafka anko shiga karan sa ya jijjiga mutane

Bidiyan matashin daya tafka anko shiga karan sa ya jijjiga mutane

A wani guntun bidiyo, an ga yadda wani matashi da kare suke kwasar rawa a cikin wata mota yayin da suke sanye da suttura iri daya, Legit.ng ta ruwaito.

Yayin da wata waka ke tashi, an ga yadda mutumin ke kambama karen yayin da karen ya cigaba da gyada kai ga kidan.

Mutane da dama sun yi mamaki yayin da suka dinga tsokaci kan yadda karen ya dinga yin abubuwa kamar mutum.

Wani @love_n_nazhas ne ya wallafa bidiyonsa da karensa a TikTok yayin da suke duk harkoki iri daya a cikin motarsa.

Tabbas saka kaya iri daya da suka yi ne ya fi komai daukar hankali kuma yadda karen ya ke bin salon wakar tamkar ya san abinda ake cewa.

Akwai wani wuri a bidiyon wanda aka ga karen ya juya kan sa zuwa tagar motar yadda mutane su ke yi.

Zuwa lokacin da aka rubuta wannan rahoton, bidiyon ya tattara tsokaci fiye da 6,000 yayin da fiye da mutane 140,000 suka yi jinjina kan bidiyon.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button