TASKAR LABARAI

Bankunan yan kasuwa sunce zasuci gaba da karban tsofaffin kudi

Zamu karbi tsofaffin kudi har wa'adi yacika Cewar Bankunan Nigeria

Gwamnan babban Bankin Ƙasa, CBN, Godwin Emefiele, ya ce bankuna za su ci gaba da karbar tsoffin  kuɗi na Naira har wa’adin musanya wa da sabbin kudi ranar 10 ga Febrairu.

Zamuci gaba da karban tsofaffin kudi har wa’adi yacika Cewar gwamnan babban banki.

Gwamnan na babban bankin ƙasa CBN Emefiele ya bayyana hakan ne gaban kwamitin majalisar wakilai kan sabon tsarin sauya fasalin Naira, da kuma canjin naira, a yau Talata, shugaban na CBN ya ce har yanzu bankuna za su karbi tsoffin takardun har bayan cikar wa’adin.

Emefiele ya ce ” sashe na 20, karamin sashe na 3 na dokar CBN ta 2007, ko da wa’adin amfanin tsoffin kuɗaɗe ya cika, CBN za ta ci gaba da karbarsu.

Emefiele ya ce dole ne bankunan kasuwanci su karbi kudin ko da bayan wa’adin na 10 ga watan fabrairu.

canji dai na sauya fasalin kuɗin ya jawo cece kuce  a cikin ƙasar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button