TASKAR LABARAI

Abun Al’ajabi Yan Sanda Sun Saki Tinkiyar Da Aka Kama Da Laifin Cin Bushasshen Kifi a Borno

Abun Al'ajabi Yan Sanda Sun Saki Tinkiyar Da Aka Kama Da Laifin Cin Bushasshen Kifi a Borno

Hukumar yan sanda a jihar Borno ta saki Tinkiyar da aka damke kan laifin cinye bushasshen Kifin wani dan kasuwa, Malam Yusuf Ibrahim, a unguwar Bulabulin Maiduguri, jihar Borno.

Mai tinkiyar, Luba Mohammed, ya bukaci dattawan unguwa su tayashi baiwa Mai Kifi Ibrahim hakuri.

Ibrahim, mai sayar da kifin da kai karar Tinkiyar caji Ofis ya bayyanawa manema labarai cewa dattawan unguwa sun bashi hakuri kuma ya hakura, rahoton Zagazola.

Amma dai ya bada sharruda wanda ya hada da kada hakan ya sake faruwa.

An saki Tinkiyar ranar Lahadi a hedkwatar yan sanda dake Bulabulin.

Bugu da kari, wani mamban kwamitin kamfen jam’iyyar APC, Hanarabul Husseini Monguno, ya baiwa mai kifin kyautar N50,000 saboda hakurin da yayi.

Laifin Me Tinkiya tayi

Tun farko dai Mai sayar da Kifi soye Malam Yusuf Ibrahim ya shigar da kara ofishin hukumar yan sanda bisa yadda tinkiyar Malam Luba Mohammed ke tafka masa barna ba kakkautawa.

Ibrahim ya bayyana cewa ya dade yana yiwa Luba gargadi bisa wannan asara da Tinkiyarsa ke janyo masa, rahoton DailyTrust.

A cewarsa, mai tinkiyar bai dawo wani mataki kan hakan ba kuma ya sa ya yanke shawarar kai kara wajen hukumar.

Kalli martanin mabiyansu a soshiyal Midiya:

Mariya M Aliyu tace:

“Nidai nace Duniyar Nan ba Gaskiya a Tuntu6i lubatu me timkiyar Nan, Anya ba lauje cikin Nadi,, ace Tinkiya harda Dan gwalar yaji”

Asmau Adam tace:

“Tirkashi dabbar ma sukunyi magana Akai lallai wannan tinkiyar kin jawo magana”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button